Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Kwamitin Gyaran Tsarin Harkokin Zaben Gwamnatin Tarayya


Zaben 2015: Ma'aikatan zabe na shrin kayan aiki

Masu fashin baki a fagen siyasar Najeriya da kungiyoyin rajin demokaradiyya da sugabanci na gari a kasar, sun fara bayyana ra’ayoyi dangane da kwamitin gyaran tsarin harkokin zabe da gwamnatin tarayya ta kafa.

Ranar Talatar da ta gabata ne dai ministan Shari’a na Najeriya Abubakar Malami, ya kaddamar da kwamitin a madadin shugaba Mohammadu Buhari.

Kwamitin wanda ke karkashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ken Nnamani. An daura masa alhakin tuntubar masu ruwa da tsaki kan yadda za a inganta lamuran zabe a Najeriya. Haka kuma kwamitin na da hurumin nazari akan rahoto da kuma shawarwarin kwamitin gyaran zabe da marigayi shugaba Umaru Musa ‘yar Aduwa ya kafa, karkashin jagorancin tsohon babban Jojin tarayya Mohammad Lawal.

Tuni dai kungiyoyin rajin dimokaradiya sukace sun daura damarar sanya idanu sosai, domin ganin gwamnati ta aiwatar da rahotan kwamitin kamar yadda ya kamata.

Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG