Accessibility links

Shugabannin Sabuwar PDP A Jihar Kaduna Sun Tsunduma Cikin APC


APC logo

Da alama jam'iyyar APC na cigaba da wawurar 'yan jam'iyyar PDP yayin da shugabannin sabuwar PDP a jihar Kaduna suka shiga APC kwansu da kwarkwatarsu.

Kamar kakar jam'iyyar APC ta yanke saka a jihar Kaduna inda shugabannin sabuwar PDP suka mikawa APC kawunansu bori ya hau.

Rahotannin daga jihar Kaduna na cewa shugabannin sabuwar jam'iyyar PDP duk sun canza sheka zuwa jam'iyyar APC. Shugaban tawagar ta sabuwar PDP Alhaji Audi Yaro Makama Rigachukun ya ce a cikin tarihin duniya ba'a taba yin jam'iyyar adawa irin APC ba.Ya ce sai da suka shirya saf kafin su fito. Basu fito yin yaudara ba ko cutar wani ba illa sha'awar Kaduna da Najeriya. Ya ce shugaba na gaya masu su daure ya ce shi ba zai zama dan adawa ba domin tun yana NEPU yake adawa amma yanzu duk inda ya je sai an ci zabe.

Shugaban rikon jam'iyyar APC na jihar Kaduna Dr. Hakim Baba Ahmed ya marabci wadanda suka canza sheka zuwa jam'iyyarsu. Ya ce sun karbesu da zuciya daya inda babu tsoro ko shakka ko tababa ko mummunan zato. Ya ce sun shigo cikin APC sun nuna cewa suna sha'awar alkiblarsu don haka an ce masu bisimilla domin a sake sabon gini. Ya ce shigowar PDP cikin APC alheri ne.

Alhaji Ahmadu Yaro Kokakola tsohon shugaban CPC a jihar Kaduna shi ne ya yi jawabi a madadin jam'iyyun da suka narke cikin APC. Ya ce sun yiwa wadanda suka shigo APC maraba sun shigo gida mai albarka. Ya ce Allah ya sa su cimma nasarar abun nan da suka hanga tare.

Isah Lawal Ikara nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG