Accessibility links

Sojojin Najeriya Sun Kai Farmaki Da Jiragen Yaki Kan 'Yan Boko Haram


Jirgin saman yaki samfurin F-16

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan Boko Haram da dama a wani gagarumin farmaki ta sama da ta kai kan wani sansaninsu

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan bindiga da dama da ake kyautata zaton 'yan kungiyar nan ce ta Boko Haram, a wani mummunan farmaki ta sama da ta kai kan wani abinda ta kira "sansanin 'yan ta'adda" a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar tsaro ta hadin guiwa a Jihar Yobe, Kyaftin Eli Lazarus, yace an kai hare-hare da jiragen saman yakin na wannan makon ne a bayan wani harin da tsagera suka kai kan Kolejin Koyon Aikin Gona ta Jihar Yobe dake Gujba a ranar lahadin da ta shige, har suka kashe dalibai 43 dake barci a cikin dare.

Lazarus ya ce an kama wasu mutane 15 da ake tsammanin su ma 'yan Boko Haram ne a lokacin wannan farmakin, kuma har sun fara bayar da bayanan da zasu iya kaiwa ga kamo sauran tsageran da suka samu sa'ar tserewa.

Yace rundunar sojojin tana nazarin wasu sabbin matakan da zata iya dauka na murkushe wannan zub da jini na kungiyar Boko Haram wadda ta ke da cibiya a yankin arewa maso gabashin kasar, inda shugaba Goodluck Jonathan ya kafa dokar-ta-baci domin shawo kan matsalar da suke haddasawa.
XS
SM
MD
LG