Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekaru 52 Bayan Rasuwar Sardauna


Sir Ahmadu Bello, (tsakiya sanye da rawani) tare da wasu turawan Birtaniya yayin wani taron samar da kundin tsarin mulki ga Najeriya da aka yi London a 1957.

Ana taruka da bukukuwan tunawa da ranar da Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello, ya rasu a sassan Najeriya. Sardauna shi ne Firmiyan farko na kuma karshe a yankin arewacin Najeriya.

Yau shekaru 52 ke nan da rasuwar Firimiyan yankin arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto, bayan wani juyin mulki da sojoji suka yi a shekarar 1966.

A Najeriya, musamman a arewaci, akan gudanar da tarurruka a sassan yankin domin yin dubi kan irin rawar da marigayin ya taka wajen hadakan kabilu daban-daban da ke yankin.

Juyin mulkin wanda aka yi a ranar 15 ga watan Janairun 1966 ya kuma yi sanadin salwantar rayukan wasu manyan mutane a kasar ciki har da Firai ministan Najeriya na farko Abubakar Tafawa Balewa.

Irin gudunmuwar da Sardauna ya bayar wajen ci gaban yankin arewacin Najeriya ya sa ya zama abin misali da kwaikwayo a sassan yankin.

Tarihi ya nuna cewa Sardauna mutum ne da ba ya nuna wariyar addini ko kabilanci ko kuma ta yanki.

Wata tambaya da ta fi jan hankulan masharhanta ita ce, shin mene ne ya sa har yanzu Sardauna ke ci gaba da zama abin kwatance da zama a zukatan mutane shekaru 52 bayan rasuwarsa?

A wannan rahoto da Murtala Faruk Sanyinna ya aiko daga Sokoto, Farfesa Bello Bada, Malami a jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto ya ba da amsar wannan tambaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG