Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Qatar Za Ta Iya Cika Sharuddan Saudiya Kafin Cikar Wa'adi?


Ministan harkokin wajen kasar Qatar Mohammad ben Abdel Rahman Al Thani yayin da yake magana da manema labarai a Paris ranar 12 juin 2017
Ministan harkokin wajen kasar Qatar Mohammad ben Abdel Rahman Al Thani yayin da yake magana da manema labarai a Paris ranar 12 juin 2017

Yau Litinin wa'adin da kasar Saudiya da wasu kawayenta suka bai wa kasar Qatar kan ta cika wasu sharudda da za ta ba su damar dawo da huldar diplomasiyya da ita zai cika, bayan da Qatar din ta nemi a kara mata tsawon wa'adin.

A yau Litinin Kasar Saudiyya da kawayenta da suka kwashe wani lokaci suna takaddama da kasar Qatar, sun kara wa’adin da suka baiwa kasar ta Qatar da sa’oi 48, domin ta cika wasu shurudda da suka gindaya mata.

A jiya Lahadi Qatar wacce ke laluben hanyoyin da za ta kawo karshen wannan takaddama da kasashen na yankin Gulf, kan yanke hulda da suka yi da ita, ta nemi karin wa’adin, jim kadan yayin da wa’adin farko da aka ba ta ke shirin cika.

Kamar yadda wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran kasar Kuwaiti da kasar ta Saudiyya suka tabbatar, an kara wa’adin zuwa yammacin yau Litinin.

Kasar ta Saudiyya da Hadaddiyar Daular Laraba da Bahrain da kuma Masar, sun ayyana yanke huldar diplomasiyya da kasar ta Qatar a ranar 5 ga watan Yuni, bayan da suka zargi hukumomin Doha da marawa ayyukan ta’addancin baya da tare da yin hulda da kasar Iran.

Qatar ta musanta wannan zargi.

Ministan harkokin wajen Qatar, Mohammed Bin Abdulrahman Al Thani, ya fada cewa bukatun da Saudaiyya da kawayenta suka gabatar, da suka hada da janye dakarun Turkiyya a Qatar da rufe gidan talbijin na Al Jazeera da tare da rage yawan hulda da kasar Iran da ba za su yiwu ba, idan har ta amsa sunanta a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG