Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Na Ziyara A Vegas Inda Wani Ya Hallaka Mutane 58


Yanzu haka shugaban Amurka Donald Trump yana ziyara a birnin Las Vegas, yayinda masu bincike a garin ke cigaba da neman dalilin da ya sa wani dan bindiga ya kai hari a wani wurin bikin raye-raye da kade-kade

Maharin ya kai wannan mummunan hari ne daga dakin sa dake benen wani Otel, inda ya kashe akalla mutane 58 da kuma kansa.

Gabanin ziyarar, shugaba Trump ya fadi cewa “za mu je mu ga wadanda suke murmurewa, da wadanda suka tsira. Ya kara da cewa, zamu kuma gana da ‘yan sanda, da shugabansu, bayan haka zamu kasance a garin na wani dan lokaci.

Shugaban na Amurka ya kuma bayyana maharin a matsayin “mara hankali,” ya kuma ce nan gaba za a tattauna akan batun sabbin dokokin mallakar bindiga.

Bayan wadanda suka rasa rayukansu, mutane fiye da 500 suka jikkata a lokacin harin.

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG