Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Zabi Sabon Mai Ba Kasa Shawara Kan Tsaro


Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da sabon Mai Ba Da Kasa Shawara Kan Tsaro, Laftana-Janar H.R. McMaster, wani kwararre kan dabarun matakan soji wanda ya dade ya na aikin soji.

Trump ya bayyana McMaster dan shekaru 54 da haihuwa da "mutum mai matukar basira da kuma sanayya ."

Da ya ke yin sanarwar a wurin shakatawarsa na Mar-a-Lago da ke gabar tekun Atilantika a Florida, Trump ya ce shi kuma Laftna-Janar Keith Kellogg, wanda shi ya yi mukaddashi kafin nan, a yanzu zai zama Shugaban Ma'aikata a Majalisar Tsaro ta kasa.

A halin yanzu McMaster shi ne Daraktan Cibiyar Habbaka dabarun aikin soji, wadda aikinta shi ne 'hada hancin dukkannin dabarun iya yaki zuwa gundarin matakin soji,' da kuma tuntubar sauran cibiyoyin gwamnati. Trump ya zabe shi bisa dauran 'yan takara uku, ciki har da Kellogg.

McMaster zai maye gurbin Michael Flynn, tsohon Janar din soji dinnan da Trump ya sallama daga aiki a makon jiya bayan ya yi kwanaki 24 kan aikin, wato tun kahuwar gwamnatin Trump mai mazauni a Washington. Sabon Shugaban ya fadi makon jiya cewa ba zai lamunta da karyar da Flynn ya yi ma Mataimakin Shugaban kasa Mike Pence ba, game da tattaunawarsa da Jakadan Rasha a birnin Washington makonni, gabanin rantsar da Trump wata daya da ya gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG