Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Zai Gana Da Shugaban Kasar China


Shugaban Amurka Donald Trump (Hagu) Da Shugaba Xi Jinping Na China (Dama)
Shugaban Amurka Donald Trump (Hagu) Da Shugaba Xi Jinping Na China (Dama)

Ranar alhamis din nan mai zuwa ake sa ran shugaba Donald Trump, zai karbi bakuncin shugaban kasar China, XI Jinping, a wurin hutawansa dake Mar-a-Largo, dake gabar teku a jihar Florida, Sai dai ana hasashen cewa wannan ganawar ba za ta yi armashi ba.

Wannan hasashen ya fito fili ne domin shugaba Trump, ya rubuta a shafinsa na twitter, cewa ba shakka ganawarsa da shugaban na China, karo na farko, tattaunawar ba za ta yi dadi ba, domin ko Amurka, ba za ta ci gaba da barin ana kwararta ba a harkar kasuwanci da take yi da kasar ta China, wanda ke sa Amurka, hasara da kuma rasa ayyukan yi ga ‘yan kasa.

A wata ganawa da shugaba Trump, ya yi a fadar White House, da masu masana’antu a anan Amurka, ya shaidawa mahalarta taron cewa za su yi sha’awar kallon yadda ganawar tsakaninsa da shugaban kasar China, za ta kasance.

"Ya ce na matsu domin in karbi bakuncin tawagar kasar China, kuma za ku ga yadda za ta kaya tsakani na da su”.

Sai dai ga dukkan alamu shugaban kasar ta China, ba zai iso hannu rabbana ba.

Haka kuma kafin wannan ganawar ta jibi mutane daban-daban kowa na fadin albarkacin bakin sa game da wannan ganawar, wadda ake shirin kallo.

Misali wasu masu kallon yadda harkokin kasar China, ke tafiya sun ce ba kome ne zai tafi kamar yadda aka tsara ba, domin ko akwai abubuwa da dama a farkon mulkin na shugaba Trump, da basa bisa tsari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG