Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Zai Yiwa Amurkawa Jawabi Kan Halin Da Kasa Ke Ciki


Donald Trump

Da Marrecen yau Talata Shugaban Amurka zai yi jawabi akan makomar Amurka.

A yau Talata ne, Shugaban Amurka Donald Trump, zai gabatar da “Halin da Kasa Ke Ciki” na wannan shekarar a gaban gangamin ‘yan Majalisar Dokokin Kasar da za su hada da dimbin wakilai mata da tsirarun jinsuna masu yawan da ba a taba gani a tarihin Majalisun ba.

Shugabar Majalissar wakilai da za ta zauna bayan Trump ita ce Nancy Pelosi, wadda ta hada kan yan Majalissar wakilai na jam’iyarta ta Democrats karkashin tuta daya wajen kin amincewa da kudirin shugaban kasar na neman makudan kudade da zai gina wata Katanga akan iyakar Amurka da Mexico, abin da ya janyo rufe mai’aikatu gwamnatin Amurka na lokaci mafi tsawo a tarihin kasar.

Trump dai zai yi Jawabin ne da jinkirin mako, da yake tun ranar 29 ga watan Janairu ya kamata ya gabatar da jawabin amma kuma sai ita Pelosi ta taka mai birki, ta ce ba za’a bar shi ya yi jawabin ba sai an bude mai’aikatun gwamnati.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG