Shugaban Amurka Donald Trump, ya fadawa taron shugabannin Kungiyar raya tattalin arzikin Asia ta APEC cewa a shirye yake ya kulla yarjejeniya da kowace kasa a yankin tekun India amma kuma yayi tsayin daka cewar ba zai kulla yarjejeniya da gungun kasashe, misali na yarjejeniyar cinikayya da kasashe 12 da aka lakabawa suna Trans Pacific Partnership, wanda Mr. Trump ya gaggauta yin watsi da ita a farko-farkon gwamnatinsa.
Shugaban na Amurka yace a baya "idan Amurka ta kauda shingayen cinikayya, wasu kasashe basa, sauran kasashe sun ki bamu damar shiga kasuwanin su."
Shugaban China Xi Jinping da gwamnatin kasarsa ce ke gudanar da galibin harkokin kasuwanci nan da nan ya biyo Trump da nasa jawabi a Da Nang.
Shi dai Xi ya yi na’am da kulla yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashe, ya kuma yi kira na a bada goyon baya ga yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen dake yankin na Pacific Asia mai lakabin FTAAP wanda zai kawo daidaito ga yarjejeniyoyin cinikayya tsakanin kasashe masu yawa, da kuma tsakanin wata kasa da kawarta.
Facebook Forum