Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Hamayyar Sudan Ta Kudu Reik Machar Yana Jinya A Khartoum


Riek Machar

Wani ministan kasar Sudan ya shaidawa VOA cewa, Shugaban hamayyar Sudan ta Kudu Reik Machar yana jinya a Khartoum.

Ministan watsa labarai Ahmed Bilal ya shaidawa VOA cewa, an kai Machar Sudan cikin wani yanayin rashin lafiya mai tsanani. Bilal yace, shugaban hamayyar yana fama da wani matsanancin ciwon kirji da kuma matsala a kafarsa, domin ya yi tafiya da kafa ta tsawon kwanaki goma sha biyar.

Yace an sanar da Juba halin da yake ciki.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya sauke Machar daga matsayinsa na mataimakin shugaban kasa, bayan sake barkewar wani sabon fada a babban birnin kasar watan jiya tsakanin dakarun dake goyon bayan abokon hamayyar. Fadan ya tilasta dubun dubatan mutane kauracewa matsugunansu.

Machar ya janye zuwa cikin jeji lokacin fadan, kuma cikin watan nan dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a damokaradiyar Jamhuriyar Congo suka samo shi da rauni a kafa. Kakakinsa ya fada tun farko cewa, Machar ya kauracewa Sudan ta Kudu ne da nufin gujewa dakarun Kiir, kuma raunin da yaji bashi da tsanani da zai bukaci jinya.

Da aka tambayeshi wanda ya raka Machar zuwa Khartoum, sai Bilal ya amsa da cewa, shi kadai ya tafi.

XS
SM
MD
LG