Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kamfanin Tuwita (Twitter), Jack Dorsey Ya Yi Murabus


Shugaban Kamfanin Tuwita (Twitter), Jack Dorsey.

Wanda ya kirkiro kamfanin Tuwita (Twitter), Jack Dorsey ya ce ya ajiye mukaminsa na shugaban kamfanin sada zumuncin Twitter.

A wata sanarwa da aka bayar, kamfanin Twitter ya ce Parag Agrawal, wanda shi ne shugaban kamfanin a fannin kimiyya tun daga shekarar 2017, shi zai maye gurbin Dorsey. Kuma matakin zai fara aiki ba tare da bata lokaci.

“Na yanke shawarar barin kamfanin Twitter saboda na yi imani kamfanin ya shirya fita daga hannun wadanda suka kafa shi. Ina da kwarin gwiwa akan Parag a matsayin shugaban Twitter. Ayyukansa cikin shekaru 10 da suka wuce sun kawo sauyi a kamfanin, abinda Dorsey ya fada kenan a wata sanarwa a jiya Lahdi. Ya kara da cewa, Ina kaunar Twitter.”

Dorsey dan shekara 45, shi ya bude kamfanin tun a shekarar 2006 kuma shi ne shugabansa har zuwa 2008 lokacin da aka maida shi gefe guda amma daga baya ya sake komawa babban mukamin a shekarar 2015.

A shekarar da ta gabata, shugabannin kamfanin Elliott dake da hannun jari a kamfanin, suka so Dorsey ya zaba tsakanin zama shugaban kamfanin Twitter ko shugaban Sqaure, wani kamfanin harkokin kudi ta yanar gizo.

XS
SM
MD
LG