Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kare Hakkin Bil'adama Ya Yi Tur Da Matakin Da Isra'ila Ta Dauka


Shugaban Hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin duniya yayi Allah wadai da kasar Isra’ila akan yadda take take hakkokin Falastinawa.

A wani zama na musamman da majalisar kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ta yi a ranar juma’a, domin tattaun kara lalacewar halin da ake ciki a yankunan da falasdinawa suke, Zeid Ra’ad al-Hussein ya ce daga rayuwarsu har mutuwarsu, mutane miliyan 1 da dubu casa’in a Gaza suna zaune ne a cikin mawuyacin halin a wasu unguwanni masu fama da masifar gubar talauci.

Zaman na musamman zai iya janyo a kafa wata hukumar bincike akan tashin hankalin da ke faruwa akan iyakar Gaza a wannan satin, wanda mutane 60 suka mutu sannan 2,700 suka raunata. A cikin wadanda suka mutu akwai mata da kananan yara wanda suka hada da yarinya yar wata 8.

Jakadan Isra’ila a cikin Hukumar kare hakkin bil adaman ta majalisar dinkin duniya yace binciken tashin hankalin Gazan ba zai canza abubuwan da ke faruwa ba ko kadan.

Tashin hankalin dai ya samo asali ne a sanadin ofishin jakadancin Amurka da aka yi ne a birnin Kudus.

Facebook Forum

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG