Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Siriya Yayi Alkawarin Yiwa 'Yan Tawayen Kasar Ahuwa


Shugaban Siriya Bashar al-Assad

Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya ce zai yi afuwa ga ‘yan tawayen kasar wadanda suka amince su ajiye makamansu, suka kuma mika kansu ga hukumomi daga nan zuwa watanni 3 masu zuwa.

Bayan yarjejeniyar afuwar kuma, Assad da ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu sun ce gwamnatocin Rasha da Siriyya zasu bude wasu hanyoyin fita birnin Aleppo guda 3 don fararen hula da yan tawayen da suka amince su ajiye makamansu, sai kuma hanya daya don yan tawayen da basu amince ba kuma suna so su gudu da makamansu.

A wani jawabi da suka yi ta kafar Talabijin, Shoigu da shugaba Vladimir Putin sun ce nan ba da jimawa ba zasu fara aikin bada agaji mai yawan gaske a wajen Aleppo don taimakawa fararen hular da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su, har ma da mayakan suka yarda su ajiye makamansu.

Bayan hanyoyin da za a bude kuma, Shoigu ya fadi cewa zasu tanadar da sansanonin bada abinci, da magunguna a wajen birnin.

XS
SM
MD
LG