Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban 'Yan Adawa Raila Odinga Ya Caccaki Amurka Da Kasashen Yammacin Turai


Shugaban ‘yan adawa Raila Odinga, yaki shiga zaben kasar kuma ya kira magoya bayan sa da su kauracewa zaben kana masu zanga-zaga sun hana bude runfunan zabe a wasu sassan da shi madugun ‘yan adawar ke da karfi sosai.

Hukumar zaben kasar Kenya ta bayyana shugaba mai ci Uhuru Kenyata a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da kusan kuri’u kashi 98.

Sai dai zaben na ranar alhamis bai samu fitowar jama’a ba domin kuwa, kasa da kashe 39 ne suka fito wato daga cikin adadin mutane muliyan 19.6 da suka yi rajistar jefa kuri’a, kamar yadda shugaban hukumar zaben kasa Wafulachi Bukati shugaban hukumar zaben ya bayyana yau littini.

Shugaban ‘yan adawa Raila Odinga, yaki shiga zaben kuma ya kira magoya bayan sa da su kauracewa zaben kana masu zanga-zaga sun hana bude runfunar zabe a wasu sassan da shi madugun ‘yan adawar ke da karfi sosai.

Zaben wanda aka sake cikin wannan watan, rusassahen da aka gudanar ne a cikin watan agusta wanda aka bayyana shugaba Uhuru Kenyata a matsayin wanda ya lashe, amma kuma babbar kotun kasar tace ta gano an tafka rashin Gaskiya a cikin sa.

Sai dai ga abinda Raila Odinga, ya shaidawa kanfanin dillacin labarai na Associated Press, cewa ’’Wannan zabe ne tsakanin Uhuru da Uhuru, kuma shugaban na nema ya bata wasu hukumomin mulkin kasar mu’’

Sai dai Odinga ya soki lamirin Amurka dama wasu jami’an diflomasiyya na wasu kasashen Turai da zamowa masu shiga sharo ba shanu domin ko sun bukaci a sake maimaita zaben na ranar alhamis.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG