Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Sun Ce Kotu Tana Nuna Wariya


Shugabannin Afirka su na tattauna batun dangantakarsu da kotun ICC a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia, 11 Oktoba 2013.

Shugabannin suka ce kotun bin kadin manyan laifuffuka ta duniya, ICC, ba ta bincike ko shari'ar kowa a duniya im ban da 'yan Afirka, wannan kuma wariya ce

Shugabannin kasashen Afirka dake taro a kasar Habasha ko Ethiopia, sun yi kira ga Kotun bin Kadin Manyan Laifuffuka ta Duniya da ta jinkirta shari’ar da take yi ma shugabannin kasar Kenya har sai zuwa wani lokaci.

Shugabannin Afirka da dama dake halartar taron kolin da Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka take yi sun bayyana damuwar cewa kotun tana nuna wariya a kan kasashen Afirka, kuma babu wadanda ta sanya a gaba in ban da ‘yan kasashen Afirka.

Firayim ministan kasar Ethiopia, Hailemariam Desalegn, wanda shi ne shugaban Tarayyar ta Kasashen Afirka mai ci a yanzu, yayi kira ga kotun da aka fi sani da lakaninta na ICC da ta kasa kunne sosai ga irin koke koken da Tarayyar da ta kunshi kasashe 54 ta gabatar.

Mr. Desalegn yace shari’ar da kotun ta ICC keyi yanzu tana hana shugabannin kasar Kenya mayarda hankali a kan batutuwan cikin gida.

Kotun ta shirya fara shari’ar shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, a watan Nuwamba bisa zargin cin zarafin bil Adama dangane da rawar da ake zargin ya taka a tashin hankalin da aka yi bayan zabe a Kenya a 2007 zuwa 2008. Mataimakinsa, William Ruto shi ma yana fuskantar irin wannan tuhuma.

Haka kuma, kotun tana neman kama shugaban kasar Sudan, Omar al-Bashir, wanda ek halartar taron na Addis Ababa, bisa zargin laifuffukan yaki da kisan kare dangi da ake zarginsa da su a yankin Darfur.

Sauran shari’o’in dake gaban kotun sun hada har da ta tsohon shugaban kasar Cote D'Ivoire, Laurent Gbagbo, wanda yake fuskantar tuhumar laifuffukan cin zarafin bil Adama.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG