Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Koriya Ta Kudu Da Arewa Sun Sake Ganawa


A karon farko Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Ketara Zuwa Koriya ta Kudu

Shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya gana da takwaransa na Koriya ta arewa Kim Jong Un yau asabar domin tattaunawa kan yiwuwar taron kolin da ake kyautata zaton gudanarwa da shugaban Amurka Donald Trump, bisa ga cewar Koriya ta Kudu, ganawar shugabannin ta biyu a cikin watanni.

Sanawar da ofishin shugaban Kasar Koriya ta Kudu ya fitar ta bayyana cewa, Moon da Kim sun gana a kan iyakar da aka girke dakaru da rana domin musayar miyau da zai bude kofar tattaunawa tsakanin Koriya ta Arewa da Amurka.

Wani Mukarrabin shugaban kasar Koriya ta Kudu ya bayyana cewa, Moon zai bayyana sakamakon tattaunawar da suka yi ta tsawon sa’oi biyu da Kim gobe lahadi da safe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG