Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Musulmai Dana Krista Sun Gudanar Da Taron Hadin Kai A Ghana


Shugabannin Musulmai Dana Krista Sun Gudanar Da Taron Hadin Kai A Ghana

Kungiyar Krista ta Ghana ta hada gwiwa da ofishin Shugaban musulman kasar don ganin cewa an gudanar da zaben kasar na wannan shekara cikin aminci da luman.

Taron ya hada shugabannin addinai a birnin Kumasi don neman tattaunawa a kan tabbatar da zaman lafiya kafin zabe da lokacin zaben har ma da bayan zaben.

Rev. Dr. Kwaben Opuni-Frimpong, shine babban sakataren kungiyar Kristan Ghana ya yi tsokaci a kan muhimmancin wannan taron yan cewa musulmi da krista sun kwashe shekaru suna aiki akan lamurra da suka shafi kasa. Har ma ya nemi ayi aiki tare don ganin zaben mai zuwa anyi shi cikin lumana.

Dr. Opuni yace akwai nasarori da dama da addinan kasar suka samu wurin hadin kai don haka dole mufahimatar da juna siyasa ba batu ne na fada ba.

Malamai da sarakai da kuma limaman coci coci duk sun halarci taron da hadin guiwan tsakanin ofishin shugaban musulmin Ghana da kungiyar Kirsta ta Ghana da aka yi a babban masallacin birnin Kumasi.

Ganin irin muhimmiyar rawa da yan jarida ke takawa a harkokin siyasa taron ya mayar da hanakali a wurin, Yussif Abdul Ganiyu Inshola na gidan Radiyon Zuria ya halarci taron kuma yayi kira ga abokan aikinsa da cewa su kasance masu gaskiya a ayyukansu.

Saura wata biyu a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘Yan Majalisu a Ghana, kuma yakin neman zabe na nan na ci gaba a fadin kasar.

XS
SM
MD
LG