Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Najeriya Da Afirka Ta Kudu Sun Kaddamar Da Tattaunawa Ta Matasa Domin Zaman Lafiya


Buhari Da Ramaphosa
Buhari Da Ramaphosa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban kasa Cyril Ramaphosa sun kaddamar da taron tattaunawa tsakanin matasan Najeriya da Afirka ta Kudu ranar Alhamis a Abuja, don samar da zaman lafiya da tsaro, ci gaban matasa da kuma shiga harkokin siyasa. 

Da yake magana da matasan ta yanar gizo, shugaba Buhari ya nuna kwarin gwiwar cewa kaddamar da taron tattaunawar na matasa zai wanzar da zaman lafiya da ci gaba, tare da taimaka wa kasashen biyu wajen magance tayar da zaune tsaye tsakanin.

Shugaban na Najeriya ya kuma lura cewa, tattaunawar za ta bai wa kasashen biyu damar bunkasa dabarun hadin gwiwa a fannonin kimiyya da fasaha, wadanda suka hada da batun sauyin yanayi, bukatun makamashi, fasahar kore, fasahar makamashi mai tsafta, tsaro ta intanet, kimiyyar sadarwa ta telematics, aikin gona. , sauran fasahohi da dai sauransu.

''Najeriya da Afirka ta Kudu suna da yawan al'umma wajen miliyan 262, wanda miliyan 95 daga cikinsu matasa ne.

''Wannan ya zamanto wata babbar dama ga ƙasashen biyu muddun za mu yi da gaske wajen amfani da wannan bangare na jama’a da daukar jajartattun matakai.

''Wannan ɗimbin adadi na matasa na kuma iya zama musabbin samun manyan matsaloli idan muka kasa haɓaka abubuwan da suke iyawa a duniya wadanda kara kusantuwa da al’ummar ke yi da kuma fasahar zamani ke saurin canza su.

''Waɗannan dalilai ne hikimar kawo shawarar bullo dawannan Tattaunawar Matasa.

“Kasashen biyu suna bukatar karin matasa masu ilimi, karin ƙwararrun matasa, ƙarin matasa a fannin kasuwanci, ƙarin masu iya samar da mafita da masu wanzar da zaman lafiya da ƙarin matasa masu kishin ƙasa.

''Gaskiya ne cewa tuni matasanmu su ka shiga haɗa kai musamman a bangaren fasahohi, suna musayar al'adunmu masu kayatarwa.

"Za mu ci gaba da yin hakan musamman a tsarin fadada harkokin kasuwanci tsakanin Afirka da muke da niyyar inganta ta hanyar yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci ta nahiyar Afirka," in ji shi.

Ramaphosa Ya Kai Ziyara Najeriya

Lokacinda Ramaphosa Ya Isa Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00

Shugaban na Najeriyar ya bayyana kwarin gwiwar cewa, hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha da sauran bangarori da dama ta hanyar dabaru da jajircewa zai samar wa kasashen biyu mafita da mallakar muhimman fasahohi da za su haifar da tattalin arzikin da zai samar da miliyoyin ayyukan yi.

“Dole ne in yi kira ga matasanmu da su rika ganin kansu a matsayin ’yan’uwa da yin tarayya a yayin amfana da abubuwa da dama da nema tare, ba kamar abokan gaba ba.

"Ko idan Bafana Bafana da Super Eagles su ka fafata, dole ne ya kasance a matsayin gogayya ta kawance," in ji Shugaba Buhari.

Shugaban na Najeriyar ya bayyana kaddamar da kwamitin gudanarwa kan tattaunawar matasa a lokacin taron kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu a matsayin wani gagarumin ci gaba.

"Taron zai yi kokarin hada kawuna wajen magance tashe tashen hankula tsakanin matasa, musanyar ra'ayi da damarmaki da kuma rage sabani a tsakaninsu," in ji shi.

A cewar shugaban bangarorin da za a hada gwiwa a karkashin tattaunawar matasan za su hada da shirye-shiryen musayar ra'ayi kan fitattun al'amuran kasa da kasa da kasa da kuma na tarihi; Shirye-shiryen hidimar matasa na kasa; raba mafi kyawun ayyuka a kan dokokin matasa na ƙasa, tsare-tsaren manufofi da jagororin da ci gaban kasuwanci da tallafi na matasa.

Sauran bangarorin da za a hada kai su ne bunkasa kasuwanci da sayar da kayaki ga matasa; Haɗin gwiwa wajen ciyar da matasa gaba a sassan da su ka hada da: ma'adinai, muhalli, kurmi, manyan dazuka da kuma tsare tsare na rage barna, in ji shi.

Daga Yarjejeniyar ta kafa Tattaunawar Matasa, musayar bayanai kan fasahohi, bincike da shirye-shiryen kowa ci gaba da bada taimako ta fannonin samun sukuni, samuwa da kuma arha na abubuwan taimakawa wajen kai komo da kazar kazar sun fito fili:

Ana sa ran kwamitin gudanarwar zai fito da jadawalin yadda za a aiwatar da Tattaunawar Matasa.

A wani karin haske kan wannan rahoton, Kakaki a fadar Shugaban Najeriya Garba Shehu, wanda ya tattauwa da Muryar, ya ce shugabannin biyu sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya don karfafa zumunci tsakanin kasashen biyu da hanyoyin da za a taimaka wa matasa wajen habbaka tattalin arziki da sauransu.

Saurari karin bayani a rahoton Umar Faruk Musa:

Shugabannin Najeriya Da Afirka Ta Kudu Sun Kaddamar Da Tattaunawa Ta Matasa Domin Zaman Lafiya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00


XS
SM
MD
LG