Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben A 'Yan Majalisa A Afghanistan Ya Huskanci Hare Hare


Masu Zabe a Afghanistan

An kashe mutane 15 kana wasu 60 sun jikata a jiya Asabar, yayin da wani dan kunar bakin wake ya yi yunkurin shiga wata runfar zabe a arewacin Kabul.

Akwai ‘yan sanda guda takwas a cikin wadanda suka mutun, wadanda suka yi kokarin tare maharin a shingen farko na jami’an tsaro inda ya tada bam din jikinsa, a cewar mataimakin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan Afghanistan Nasaratullah Rahimi.

Rahotanni sun ce zaben ‘yan majalisar dokoki na jiya Asabar a Afghanistan ya huskancin hare hare a fadin kasar, yayin da kuma rahotannin suka ce an samu dogayen layin miliyoyin mutane da suka kada kuru’unsu.

Kungiyar Taliban ta yita bada kashedin kai hare hare a kan runfunan zabe da duk wasu harkokin zabe a kasar. Sai dai wannan barazana bai hana dimbin mutane fitowa su kada kuru’unsa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG