Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar Uban Gida Tana Da Hadari Ga Damokaradiya:Masana


ADAMAWA: Jerin masu neman yin rajistan zabe da nakasassu
ADAMAWA: Jerin masu neman yin rajistan zabe da nakasassu

Masana harkokin siyasa sun nuna damuwa dangane da abinda suka bayyana a matsayin dutsen tuntuben siyasa da ya shafi jingina ga masu hali ko ikon fada aji a tsarin damokaradiya.

Yayin da ‘yan siyasa a Najeriya da jam’iyyun su ke daura damarar fafatawa a babban zaben kasar da zai gudana a watan fabarerun badi, masu ruwa da tsaki a fagen siyasar kasar na ci gaba da fashin baki dangane da yadda akida da tsarin uban gida a harkokin siyasar kasar.

Siysar uban gida a najeriya, wani al’amari ne dake ci gaba da daukar sabon salo a kasar.

Yadda jam’iyyu APC da PDP suka gudanar da zabukan fitar da gwani na ‘yan takarar gwamna dana ‘yan majalisar dokoki da kuma korafe korafen da suka biyo baya ya kara haska mummunan tasirin sisayar uban gida a najeriya.

Zaben fitar da ‘yan takarar gwaman Lagos a Jam’iyyar APC dana jihar Kano a jam’iyyar PDP na daga cikin dinbin misalan yadda jam’iyyun suka yi zabukan su na cikin a bana. Abinda masu kula da lamura suka ce zai iya haifar da gagarumar matsala nan gaba, ganin yadda sau da dama wadanda ake kira “uban gida” suke dagewa kan wanda suke so, ko da kuwa jam’iyar da kuma sauran magoya bayanta basu ra’ayinshi.

Da damai dai ‘yan najeriya na cewa, siyasar uban gida na daga cikin manyan dalilan dake hana ‘yan majalisar dokoki ta kasa tabuka abin kirki a zauren majalisar.

Saurari Cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari

Siyasar Uban gida a Najeriya-3:33"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG