Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kame Shugaban Mali, Firayim Minista Da Ministan Tsaro


BAH NDAW
BAH NDAW

A jiya Litinin jami’an sojan kasar Mali suka tsare shugaban kasa da Firai Minista da kuma ministan tsaro na gwamnatin wucin gadi.

Lamarin dake kara dagula sha’anin siyasa watannn baya juyin mulkin sojoji da ya hambarar da tsohon shugaban kasa, a cewar majiyoyi da dama suna fadawa kamfanin dillancin labaran Reuters.

An kwashe shugaban kasa Bah Ndaw, firai minister Moctar Ouane da kuma minsitan tsaro Souleymane Doucoure zuwa tungar soji a Kati a wajen babban birnin kasar Bamako, sa’o’i bayan wasu manyan sojoji biyu sun rasa mukaman su a wani garanbawul da gwamnati tayi a cewar wata majiyar diflomasiya da ta gwamnati.

Moctar Ouane
Moctar Ouane

Tsare sun ya na zuwa ne bayan da sojoji suka hambarar da shugaba Ibrahim Boubacar Keita a cikin watan Agusta. Lamarin dake faruwar ka iya kara rashin zaman lafiya a kasar dake Afrika ta Yamma inda kungiyoyin ta’addanci masu alaka da al Qaida da IS ke rike da ikon wurare da dama a saharar arewacin kasar.

Tabarbarewar sha’anin siyasa da rikici tsakanin sojoji yana gurgunta kokarin da shugabanni da kasashe makwabta ke yi domin kyautata halin da kasar mai fama da talauci ke ciki, wadda take kuma taka rawa wurin tabarbarewar tsaro a yankin.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali ya yi kira ga sojoji da su saki shugabannin bada bata lokaci ko sharadi ba kana yace duk wadanda suka kama su za a hukuntasu a kana bin da suka aikata.

XS
SM
MD
LG