Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Fatattaki 'Yan Boko Haram

Sojojin Najeriya. (File Photo)
Sojojin Najeriya. (File Photo)

‘Yan kungiyar Boko Haram, sun sake wani sabon yunkuri na shiga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ta bangaren kudu, amma sun gamu da tirjiya daga Sojojin Najeriya.

‘Yan kungiyar Boko Haram, sun sake wani sabon yunkuri na shiga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ta bangaren kudu, amma sun gamu da tirjiya daga Sojojin Najeriya.

Sojojin da taimakon ‘yan kato da gora sun dade suna bata kashi da ‘yan kungiyar ta Boko Haram, a yankin Mulai, kimanin kilomita uku, kudu da garin Maiduguri, wanda daga bisani suka fatattake ‘yan kungiyar ta Boko Haram.

A makon da ya wuce ma ‘yan Boko Haram, sun yi yunkurin shiga Maiduguri, rundunar Sojojin Najeriya, ta ce zata aika da dakaruta zuwa arewacin Maiduguri, domin harin da aka kai ta kudancin yana iya kasancewa wata dabara ce, ta yaki.

XS
SM
MD
LG