Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Somalia sun kashe wasu mayakan sa kai na kungiyar al-Shabab


Yankin Galgudud na Somalia da sojoji suka kai samame

Sojojin Somalia da ke yaki da ta’addanci sun kashe akalla wasu da ake zargin ‘yan yakin sa kan ‘yan ta’adda ne guda goma sha biyar a wani samamen da aka kai sansanin ‘yan Al-Shabaab da ke yankin Gulgudud a tsakiyar kasar, makamancin samame na biyu a cikin kwanaki biyu.

Wani jami’in karamar hukuma mai suna Qadar Mohamed Ali ya fadawa sashin Somali na Muryar Amurka cewa, manufar wannan samamen shine tarwatsa sansanin ‘yan ta’addan ta yadda za a dakilesu daga shirya kai hare-harensu a cikin kasar.

Ali yace, sojojin na Somali sun kwace na’urorin harba bam da wasu makaman dangin bindiga. Ya kara da cewa ba wani Sojan rundunar da aka kashe ko kuma aka jikkata a samamen.

Samamen da ya biyo baya kwana daya da kai wani samamen a sansanin ‘yan Al-Shabaab da ke kauyen Toratorow, mai nisan tazarar kilomita 100 daga Kudu maso Yammacin Mogadishu babban birnin kasar.

Gwamnatin kasar na fama da yakar ‘yan Al-Shabaab tun lokacin da aka kafa kungiyar ta’addancin mai alaka da ta Al-Qaida a shekarar 2006. A shekarar 2008 ne Amurka ta bayyana Al-Shabaab a matsayin kungiyar ta’adda, sannan suka karfafa Somalia da taimakon kudi da na soji don murkushe ‘yan ta’addan.

XS
SM
MD
LG