Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sufeto Janar Na 'Yan Sanda Ya Bada Umarnin Gurfanar Da Wata Lauya Da Taci Zarafin Yarsanda A Abuja


Farfesa Zainab

Ana zargin farfesa Zainab Dinne da wata mai mata aikin gida Rebecca Enechido da kuma wani mutum da laifin cin mutuncin 'yar sandar da raunata ‘yar sanda mai tsaron lafiyarta.

Lamarin dai ya faru ne a ranar talata ashirin ga watannan na satumba a gidanta dake Garki a tsakiyar birnin Abuja bayan jami'ar 'yarsandar taki sabawa ka'idojin aikinta na gudanar da ayyukan gida wanda ba shine aikinta ba.

Farfesa Zainab da mai aikinta
Farfesa Zainab da mai aikinta

Sufeta Janar na 'yansandan Najeriyar Usman Baba wanda yayi Allah wadai da cin mutuncin 'yar sandan, kazalika ya bada umarnin gurfanar da wadanda ake zargin wadanda a halin yanzu suke tsare a hanun 'yan sandan ganin binciken farko ya nuna sun taka rawa wajen raunata jami'ar 'yar sandan.

Shugaban 'yan sandan Najeriyar kazalika ya kuma bada umarnin kamo daya mutumin da aka hada kai dashi wajen cin mutuncin jami'ar tasu a duk inda yake buye don shima a gurfanar dashi a gaban shari'a.

Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya CSP Muyiwa Adejobi ya aikewa sashin Hausa na Muryar Amurka na nuna cewa, wacce ke bi tana amfani da sunan shugaban ‘yan sandan da Iyalansa, ko kadan bata da wata alaka ta kusa ko ta nesa da ‘yan sanda, ba kamar yadda ake yadawa a kafofin sada zumunta na intanet ba.

Sufeto Janar din wanda ya nemi a janye dukkan jami'an 'yan sandan dake kare wannan lauyar, ya nuna mamakin ganin wacce ke ikirarin kare hakkin dan Adam ce kuma ta tafka wannan aika aika na cin zarafin wacce ke kareta.

Wannan al'amari dai ya tabbatar da zargin da ake yi na yadda wasu jami'an 'yan sandan ke kasancewa tamkar boyi boyi a gidajen manyan mutane da suke samarwa tsaro.

A Najeriya dai an sha ganin ‘yan sandan dake kare manyan mutane musamman ‘yan siyasa na zama tamkar yan aikin gida inda wani lokacin iyalan manyan mutanen ke sanya 'yan sandan wasu ayyukan da basu da alaka da tsaro.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG