Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Super Eagles Ta Daina Wasanta Na Neman Gurbin Gasar Afrika-Ogu


Kungiya Wasan Najeriya.
Kungiya Wasan Najeriya.

Dan wasan tsakiyar Najeriya John Ogu ya yi kira ga kungiyar Super Eagles da su fasa yin wasansu na gaba domin nuna kalubalantar gwamnatin kasar.

Ogu mai shekaru 26, ya ce kin yin wasan shima wani Magana ne.

Shima dan wasan gaba na Manchester United Odion Ighalo a ranar Talata ya kwatanta gwamnati Najeriya da abin kunya ga duniya.

Matasa sun kwashe makwanni da dama suna gudanar da zanga zangar neman rusa ‘yan sandan SARS dake yaki da fashi da makamai da miyagun ayyuka a Najeriya.

Sojojin Najeriya sun musunta zargin kisan masu zanga zangar kana shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi kira ga masu zanga zangar su kawo karshnta kana su koma kan teburi da gwamnati.

Najeriya tana da wasan shiga gasar cin kofin Afrika a watan Nuwamba, amma a cewar Ogu koda kasar ta rasa gurbinta a gasar cin kofin Afrika, zai zam tamkar sakamakon ayyukanta.

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG