Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Osimeh Na Cikin 'Yan Wasan Super Eagles Da Za Su Kara Da Saliyo


Shugaba Buhari Tare Da Kungiyar Kwallon Kafa Na Kasa Super Eagles.
Shugaba Buhari Tare Da Kungiyar Kwallon Kafa Na Kasa Super Eagles.

Dan wasan Super Eagles da ya taka rawar gani a wasannin shiga gasar cin kofin Afrika, Victor Osimeh, shi ne na farko a jerin sunayen ‘yan wasa da kocin Najeriya Gernot Rohr ya gayyace su domin karawa da Sierra Leon a wasan cancantar shiga gasar cin kofin Afirka.

Osimeh bai samu yin wasannin zumunci da Najeriya ta yi da Tunisia da Algeria ba saboda dalilai da suka shafi lafiyarsa amma dan wasan gaba na Napoli ya dawo don ya taimakawa kasarsa.

A ranar Alhamis ne Rohr ya fitar da jerin sunayen ‘yan wasan Super Eagles 24, da suka hada da kyaftin Ahmad Musa da dan wasan baya William Ekong da mai wasa a tsakiya Oghenekaro Etobo domin fafatawa da Leone Stars ta kasar Sierra Leon a cikin watan Nuwamba.

Shugaba Buhari Tare Da Kungiyar Kwallon Kafa Na Kasa Super Eagles
Shugaba Buhari Tare Da Kungiyar Kwallon Kafa Na Kasa Super Eagles

Ga Jerin Sunayen 'Yan wasan Na Najeriya Da Aka Fitar

Masu tsaron gida: Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs, South Africa); Sebastian Osigwe (FC Lugano, Switzerland); Maduka Okoye (Sparta Rotterdam, The Netherlands)

‘Yan wasan baya: Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Leon Balogun (Glasgow Rangers, Scotland); Chidozie Awaziem (FC Boavista, Portugal); William Ekong (Watford FC, England); Olaoluwa Aina (Fulham FC, England); Jamilu Collins (SC Padeborn 07, Germany); Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England); Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal); Kevin Akpoguma (TSG 1899 Hoffenheim, Germany)

Masu wasa a tsakiya: Oghenekaro Etebo (Galatasaray, Turkey); Tyronne Ebuehi (FC Twente, Netherlands); Frank Onyeka (FC Midtjylland, Denmark); Joseph Ayodele-Aribo (Glasgow Rangers, Scotland)

APTOPIX Russia Soccer WCup Nigeria Iceland
APTOPIX Russia Soccer WCup Nigeria Iceland

‘Yan wasan gaba: Ahmed Musa (Unattached); Alex Iwobi (Everton FC, England); Emmanuel Dennis Bonaventure (Club Brugge, Belgium); Moses Simon (FC Nantes, France); Samuel Chukwueze (Villarreal FC, Spain); Victor Osimhen (Napoli FC, Italy); Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Chidera Ejuke (CSKA Moscow, Russia)

Ragowar ‘yan wasa: Francis Uzoho (APOEL Nicosia, Cyprus); Samson Tijani (TSV Hartberg, Austria); Abdullahi Shehu (Omonia Nicosia, Cyprus); Ramon Azeez (Granada CF, Spain); Kelechi Nwakali (SD Huesca, Spain); Ikechukwu Ezenwa (Heartland FC); Paul Onuachu (KRC Genk, Belgium)

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG