Accessibility links

An Saki Amurkawa Biyu Da Ake Garkuwa Dasu A Najeriya

  • Aliyu Imam

An Saki Amurkawa Biyu Da Ake Garkuwa Dasu A Najeriya

Ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ya bada labarin an saki Amurkawan nan biyu da aka kama a gabar ruwan Najeriya cikin watan jiya.

Ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ya bada labarin an saki Amurkawan nan biyu da aka kama a gabar ruwan Najeriya cikin watan jiya.

Yau jumma’a ofishinn jakadancin ya gaskanta wan nan labari amma bai bada wani karin bayani ba.

Ranar 17 ga watan Nuwamba ne wasu ‘yan bindiga suka kama Amurkawan biyu da wani dan kasar Mexicon cikin wani jirgin ruwa da kamfanin Chevron ya dauki hayarsa. Ofishin jakdancin bai yi bayani ko an saki dan kasar Mexicon ba.

Mayakan sakai da wasu bata gari jiddin suke auna hare hare kan kamfanonin aikin mai da ama’aikatansu a Najeriya, kasar da ta fi ko wacce mai a nahiyar.

Bugu da kari kuma an sami karin yawan ‘yan fashi cikin teku a gabar ruwan Najeriya da wasu kasashe dake gabar teku da ake kira ta Guinea.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG