Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tabbacin Kashe Sojojin Nijar Arba'in Da Shida


Muhamadou Issoufou

A ranar lahadi ne dai aka sami labarin yadda wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne a kan kwale-kwale masu inji suka farwa Sojojin Nijar a tsibirin tafkin Karamga suka karkashe wasu da dama.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da cewa an kashe sojojinta guda 46 da kuma fararen hula 28 a karshen makon da ya gabata bayan da dakarun kasar suka fafata da mayakan Boko Haram a kokarin kubutar da wani tsibiri da ke yankin tafkin Chadi.

Jami’an tsaro sun ce sun kashe mayakan ta’addar guda 156 a arangamar da suka yi, wacce ta faru bayan da kungiyar Boko Haram ta kai wani farmaki a tsibirin Karamga a ranar asabar da ta gabata wanda dakarun kasar Nijar din suka ce tuni sun kwato ikon tsibirin.

Kwanan nan kasashen Nijar da Najeriya da Chadi da kuma Kamaru, suka kaddamar da wani samame akan ‘yan kungiyar. ‘Yan kungiyar Boko Haram sun yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu goma da kuma raba fiye da mutane miliyan daya a Arewacin Najeriya da muhallansu.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG