Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddamar Binne Tsohon Shugaban Kasar Philippines


Biyo bayan takaddamar da ake a Philippines na cewa ko za a iya binne tsohon shugaban kasar Ferdinand Marcos, kan cewa ko za a iya binne shi a makabartar zaratan kasar.

A yau Talata kotun kolin kasar Philippines ta ta yanke hukuncin cewa za a iya binne tsahon shugaban da yayi mulkin kama karya a kasar, Ferdinand Marcos a makabatar zaratan kasar.

“Babu wata doka da ta hana binne shi a awajen” a cewar mai magana da yawun kotun a lokacin da yake magana da manema labarai.

Marcos ya shugabancin ‘yan kasar daga shekarar alif dari tara sittin da biyar zuwa alif dari tara da tamanin da shidda. Mulkinsa na shekaru 20 yayi suna wajen yaduwar cin hanci da rashawa, da muzanta hakkokin jama’a don murkushe ‘yan adawa.

A watan Fabarairu na shekarar aluf dari tara da tamanin da shidda akan dole Marcos ya sauka daga mukaminsa, a lokacin da aka yi wasu zanga-zanga biyo bayan zaben shugaban kasa da aka yi mai cike da magudi, abinda ya sa akan tilas Marcos da iyalinsa tserwa daga kasar zuwa nan Amurka.

An zargi Marcos da matarsa Imelda da kwashe biliyoyin dalilin kudi, dukiyar gwamnatin kasar zuwa wani wuri.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG