Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashe Tashen Hankula Ya Tsananta A Jihar Rivers


Abinda ke faruwa yana da ban takaici ganin yadda mutane ke ci gaba da kashe kansu abinda ake alakanta shi da siyasa.

Tashe tashen hankula dai a jihar Rivers, al’amari ne daya tsananta kafin da kuma bayan zabubbuka shekara ta 2015, kuma tun bayan zabubbukan ne aka yi ta samun tashin tashina tsakanin ‘yan siyasa da ‘yan kungiyoyi asiri da ‘yan banga da dai sauransu, kuma rayuka da dukiyoyin da dama sun salwanta.

Sassan da aka fi samun wadannan tashe tashen hankula da kuma ya haifar da yin kaura ta dole ga jama’ar sassan zuwa wuraren da suke ganin cewa tudun mun tsira ne sun hada da garin Omoku da karamar hukumar Ahoada ta arewa da Emele da kuma yankin Ogoni.

Batun baya bayan nan dai wanda ya dauki hankali matuka shine na arangamar wasu kungiyoyi da suka faru wanda ya kai ga kashe mutane kusan ashirin a karamar hukumar Tai dake yankin Ogoni, kuma kididdigar jami’an tsaro shine cewar an kasha mutane goma sha hudu.

Kwamishinan rundunar ‘yan Sandan jihar Rivers, Ahamad Zaki, yace ‘yan Sanda da sauran jami’an tsaro na aiki hannu da hannu kuma an samu an kama mutane da dama kuma sassan da aka fi samun matsalar wadannan ‘yan kungiyoyi shine Ahoada, kuma abin takaici shine mutanen gari daya ne suka rabu kasha biyu.

Wani dan jihar Rivers, Mr. Dicks Saroni, yayi tsokaci akan tashe tashen hankulan ‘yan kungiyar asiri ne, yana mai cewa abun takaici ne abinda ke faruwa na yadda mutane ke ci gaba da kashe kansu kuma da dama na alakanta tu’annatin ne ga harkokin siyasar jihar ta Rivers.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG