Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Jiran Trump Ya Sanar Da Hukuncinsa Kan Yarjejeniyar Paris


Shugaba Donald Trump na Amirka yace yau Alhamis din nan idan Allah ya yarda zai bada sanarwar shawarar daya yanke, akan ko ya fitar da Amirka daga yarjejeniyar tarihi da aka kula a Paris a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar akan yanayi ko kuma a’a.

Sakon daya sa a dandalinsa na twitter, shugaba Trump yace zai bada sanarwar shawarar daya yanke da misalin karfe uku na yamma agogon Washington DC.

A lokacin da ya baiyana da Prime Ministan Vietnam wanda yake ziyarar nan Amirka, Mr. Trump yaki ya bada amsa ga tambayar da aka yi masa akan wannan batu, illa kawai, yace nan bada jimawa ba za’a san matakin da zai dauka.

Tuda farko yace yana jin bayanai daga bangarori da dama a saboda haka zai yi nazari tukuna.

Ta wani gefen kuma, shugaban na Amirka ya kara cacakar binciken da Majalisar dokoki take yi akan alakar yakin neman zaben sa da Rasha, yana ikirarin cewa yan jam’iyar Democrats ta masu hamaiya sune suka hana a saurari sheda daga wani tsohon mukarabinsa da zai wanke shi.

Mr Trump yace ba tare da bada wata sheda ba, yan jam’iyar Democrats da suke cikin kwamitin leken asiri na Majalisar wakilai basu son Carter Page tsohon mai bashi shawara akan yakin neman zabe ya bada sheda.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG