Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Na Kara Caccakar Masu Sukarsa


Donald Trump

Shugagan Amurka Donald Trump na cigaba da dulmuya cikin abin da masu sukarsa ke kira take-taken nuna banbancin launin fata, inda ya auna birnin Baltimore mai rinjayen bakaken fata, da kuma wani fitaccen mai wakiltar birnin a majalisar dokokin tarayyar Amurka mai suna Elijah Cummings,

Cummins shine ke jagorantar wani kwamiti mai matukar tasiri a majalisar wakilai, wanda ke kokarin gano sadarwar waya da aka yi ta yi tsakanin jami'an Fadar White House, ciki har da iyalin Shugaban kasa.

Wani fasto na darikar Baptist mai suna Al Sharpton, wanda wani dan rajin kare 'yancin dan adam ne mai yawan sukar Shugaba Trump ta gidajen talabijin, shi ma ya gamu da fushin Shugaba Trump din, wanda ya tabo shi a wani sakon Twitter da ya tura da safiyar jiya Litini.

Ya ce, "Shi dai Trump kamar yaro ya ke. Muddun aka tsangwameshi, to sai ya rama. Ya kara da cewa, "Bai da juriya, kuma bai da sahihin balaga," a cewar Al Sharpton a garin Baltimore. Ya kara da cewa, "Ya na ma da wata tsana ta musamman ga bakaken fata da sauran jinsinan da ba Turawa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG