Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump na kokarin samun galaba akan duk wata bita da kulin jam'iyyar Rebuplican


Donald Trump
Donald Trump

Hashakin attajirin dake neman jam'iyyar Republican ta tsayar dashi tsayawa takarar shugaban kasa Donald Trump yana kokarin tabbatar da hakan ya faru duk da zargin zangon kasan da yace shugabannin jam'iyyarsa ke yi masa

A cigaba da neman zabe Donald Trump yace yana nan kan bakarsa akan batun bakin haure cewa bai sake ra'ayinsa ba.

Wani mai taimakawa attajirin ta shirya kemfen dinsa Paul Manafort ya gayawa shugabannin jam'iyyar makon jiya cewa attajirin yana bin shirin da aka yi ne kan yadda zai yi kemfen amma mutumin zai fito fili yadda yake kaman 'yan takara da aka saba ji aka kuma saba gani.

To saidai hamshakin attajirin ya shaidawa magoya bayansa ranar Asabar a jihar Connecticut cewa bashi da niyyar sauyawa ko sake manufofinsa musamman batun hana musulmai shiga Amurka na dan wani lokaci da kuma batun gina katanga tsakanin Amurka da kasar Mexico.

Yace "kun san abu mai sauki ne na yi magana irin ta mai neman zama shugaban kasa tamkar dan siyasa. Saidai duk abubuwan da na ce zan yi sai na yisu" inji Trump.

Trump wanda ya taba gabatar da shirye-shiryen nishadi a kafar talibijan bai taba rike wani mukamin siyasa ba. Yace a fafutikar neman zabe "dole ne na dinga cika baki tare da buga kirji. Dole na cigaba da baku sha'awar saurare na in ba haka zaku yi barci ko ku watse ku barni,ko ba haka ba?" inji Trump.

Ya sake jaddada masu cewa duk abubuwan da ya yi masu alkawari zai yisu.

To saidai babban mai hamayya dashi Sanata Ted Cruz na jihar Texas yace Trump na rudan mutane da furucinsa ne. Yace makaryaci ne..

Gobe ne idan Allah ya kaimu 'yan takarar zasu fafata a jihohin Pennsylvania, Rhode Islan, Connecticut, Maryland da Delaware. Masu bin ra'ayin jama'a sun nuna Trump ne zai lashe jihohin biyar lamarin da ka iya bashi isassun wakilai da zasu sa ya zama zakara a zaben fidda gwani na jam'iyyar Republican da za'a yi a watan Yuli a birnin Cleveland dake jihar Ohio

XS
SM
MD
LG