Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Jaddada Bukatarsa Ta Gina Katanga Tsakanin Amurka Da Mexico


Trump

Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Asabar ya ci gaba da nanata shawararsa ta gina katanga a kan iyakar Amurka da Mexico, yayin da dakatar da wani bangaren gwamnatin Amurka ya shiga kwana na cikon takwas, lamarin da ya biyo bayan ja-in-ja a kan kudin aikin gina katangar.

A wani sakon Twitter da ya aike a jiya Asabar, Trump yace ‘yan Democrat su dau matakin da ya dace domin kawo karshen dakatar da gwamnatin, yana mai cewa, ina nan a cikin fadar White House ina jirar 'yan Democrats su zo mu zauna kuma mu tattauna a kan tsaron iyaka.

Ana ci gaba da samun ja-in-ja tsakanin Trump wanda yake neman dala bilyan biayr ya gina Katanga da ‘yan majalisar Democrats wadanda suka bada shawara a kan karfafa tsaron baki daya iyakar amma kuma suka kalubalnci gina katangar.

A wasu jerin skawannin Twitter a ranar Juma’a, Trump ya yi barazanar rufe kan iyakar kawata-kwata kana yace zai yanke taimako da Amurka ke baiwa kasashen Honduras da Guatemala da kuma El Salvador, idan majalisun tarraya suka ki bashi kudin gina katangar. Ya kuma yi kira da a sake dokar bakin hauren kasar da ya kira abin dariya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG