Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Sake Caccakar Mata 'Yan Majalisa Na Democrats


Trump

'Yan majalisu dokokin Amurka guda hudu na Jam’iyar Democrats sun bayyana gaban manema labarai, a wani matakin bai daya na nuna jajircewa da yin tir da caccakar su da Shugaba Donald Trump ya yi ta kafar sada zumunta da kuma ta baka.

Ya kaddamar da suka ta salon wariyar launin fata akan zabbabun yan majalisun wakilai guda hudu, wadanda dukkansu mata ne kuma 'yan tsirarun jinsi” a cewar Ilham Omar yar jam’iyyar democrats daga Jihar Minnesota wacce aka haifa a kasar Somalia kuma ta zama 'yar kasar Amurka, ta kuma kara da cewa wannan ajandar masu ra’ayin fifita jinsin farar fata ne a kasa.

Trump ya sake wallafa wasu kalaman adawa a shafinsa na twitter inda yace dukkanni 'yan majalisu hudu su koma kasashen su da rikici da talauci yayi masu katutu, duk kowa da cewa ukku cikin su yan asalin Amurka ne.

Biyu daga cikin matan wato Omar da Tlaib, sun kasance Musulman farko a majalissar dokokin Amurka kuma sunyi kiran da tsige Shugaba Trump.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG