Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Bunkasa Fanin Tsaron Amurka


Donald Trump na jawabi a tashar jirgin ruwa dake jihar Virginia.
Donald Trump na jawabi a tashar jirgin ruwa dake jihar Virginia.

Shugaban Amurka Donald Trump yayi alkawarin bunkasa fannin tsaro na Amurka.

Shugaban yayi wannan kalamin ko lokacin da ya ziyarci tashar jirgin ruwa dake Virginia, domin duba jirgin ruwan da aka kera mafi tsada.

Donald Trump din wanda yake sanye da rigar soja da kuhular soja hana salla, ya zagaya cikin jirgin na yaki, mai suna USS GERALD R FORD, Wanda aka ce an kyera shi akan kudi kusan dala biliyan 13, sai dai ance yawan kudin da aka kyera wannan jirgi ya haifar da tsaiko wajen kaddamar shi, amma ana fatan ayi hakan cikin wamnnan shekaran.

Shugaba Trump yayi anfani da wannan damar domi bayyana manufar kasafin kudin sa akan harkokin tsaro.

Domin a cikin jawabin sa na hadin gwiwa tsakanin ‘yan majilisar dokokin kasar guda biyu, yace muddin ana son ganin an wdata Amurka da tsaro to tilas ne a samar wa maza da matan dake sanye da kayan sarki kayayyakin aikin da suke bukata.

Yace ta hakan ne kawai za a samu zaman lafiya.

Yace ba mamaki ba dole ne muyi anfani da karfi ba, amma kuma muddin suka bari mukayi to su kwana da sanin cewa suna cikin hadari, Haka kuma shugaban ya zagaya wurin da direbobin jirgin ruwan suke da kuma jamian sojoji.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG