Accessibility links

Tsohon gwamnan Jihar Legas Brigediya Janaral Buba Murwa mai ritaya kuma jigo a jam'iyyar APC a Jihar Adamawa, ya canza sheka ya koma Jam'yyar PDP.

Wannan matakin ya biyo bayan wani taro ne da yayi da magoya bayan sa a birnin Yola babban birnin jihar Adamawa inda ya zargi shuwagabanin kungiyar na riko a jihar da kasancewa 'yan koren gwamnan jihar Murtala Nyako.

Buba Marwa yace “ Idan ka shiga gidan wani ai zaka gabatar da kanka a zauna ayi shawara, domin yanda za’a zo tafiya ta zamo daya, amma inna tabatar maku kawo yanzu duk kokarin da nayi domin in ga gwamna ya ci tura.”

Wani mai baiwa gwamna shawara Alhaji Ahmed Lawal ya musanta zargin da tsohon gwamna yayi, yace "ko a wajen raba mukamai raba dai-dai akayi, da kuma cewa ai dama mun san cewa bazai tsaya a jam'iyyar APC ba.”

Wani manazarcin siyasa Dr. Ahmadu Kaftin yace yanda ‘yan siyasa ke yawan canja sheka manuni ne cewa kansu kawai sukewa saboda haka ya kamata talakawa su guje su.
XS
SM
MD
LG