Ofishin Erdogan ya ce shugaban ya tattauna da shugaban Amurka Donald Trump ta wayar tarho a jiya Lahadi, kwanaki bayan da ‘yan kungiyar IS suka kai hari a birnin da ya kashe mutane 19 ciki har da sojojin Amurka guda uku da wani dan kwangila a ma’aikatar sojin Amurka.
Erdogan ya fadawa Trump cewa harin wani takala ne da ya biyo bayan shawarar Trump na janye sojojin Amurka daga Syria.
Sai dai Fadar White House bata ambaci bayanan Erdogan dalla-dalla a kan Manbij ba, amma ta ce shugabannin biyu sun amince su ci gaba da tattaunawa a kan samar da matsalaha a yankin arewa maso gabashin Syria wanda bangarorin biyu suka amince akwai matsalar tsaro.
Facebook Forum