Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UNICEF Za Ta Tura Allurar Ragakafin COVID-19 Ta J&J Miliyan 220 Zuwa Mambobin Tarayyar Afirka


J&J VACCINE
J&J VACCINE

UNICEF ta ce a ranar Alhamis din nan ta sanya hannu kan yarjejeniyar samar da allurar rigakafin COVID-19 ta Johnson & Johnson har miliyan 220 ga kasashe mambobin Tarayyar Afirka nan da karshen shekarar 2022.

Kungiyar ba da agaji ta yara ta sanar ne a cikin wata sanarwa cewa an cimma yarjejeniyar tare da J & J da ke kasar Belgium.

Za a iya kai karin wasu allurai miliyan 35 na allurar rigakafin zuwa kasashen kungiyar Tarayyar Afirka mai mambobi 55 a karshen wannan shekarar kuma za a iya yin odar wasu allurai miliyan 180 a karshen shekara, in ji UNICEF.

“Dole ne kasashen Afirka su sami wadataccen hanyar samun allurar rigakafin COVID-19 cikin gaggawa. An samu rashin adalci wajen samar da rigakafin, tare da kasa da kashi 1 cikin 100 na yawan mutanen nahiyar Afirka a halin yanzu da suka samu yin allurar rigakafin COVID-19.

Wannan ba zai ci gaba ba a haka, ”in ji Babban Daraktan UNICEF Henrietta Fore. "UNICEF, tare da dadadden tarihin ta na isar da alluran rigakafin a duk duniya, tana tallafawa kokarin allurar rigakafin COVID-19 na duniya ta hanyar AVAT, COVAX, da sauran hanyoyin don kara wadata da kuma samun alluran."

Allurar rigakafin ta J&J ta sami amincewar gaggawa daga Hukumar Lafiya ta Duniya a watan Maris.

XS
SM
MD
LG