VOA60 DUNIYA: A takaitattun labaran duniya na yau 'yan gudun hijira daga yankin Tigray na Habasha sun ce sun ga ana kashe mutane akan titi sannan sun ji karar harbe-harbe, Habasha ta bayyana rikicin a matsayin matakin tabbatar da doka a kasar, da wasu sauran labarai.