Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Bincike Ya Musunta 'Yan Gudun Hijira Na Shiga Da Cuta Turai


Ma'aikatar lafiya

Wani sabon rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar ya banbanta da bayanan farko da ke cewa ‘yan gudun hijira suna shiga kasashen Turai dauke da cututuka da ake iya yadawa.

Rahoton da aka buga bayan bincike takardun bayanai dubu goma sha uku ya tarar cewa, ‘yan gudun hijira suna barin kasashensu cikin koshin lafiya, amma rashin kyau yanayi, na iya sawa su kamu da rashin lafiya lokacin da suke neman mafaka ko kuma yayinda suka isa kasashen da suka karbesu.

Darektan shiya ta hukumar Lafiya ta Duniya a kasashen Turai, Zsuzsanna Jakab ta shaidawa Muryar Amurka cewa, rasa matsugunansu kadai barazana ce ga lafiyar ‘yan gudun hijiran.

‘Yan cirani da ‘yan gudun hijiran da suke zuwa kasashen Turai, basu shigowa da cututukan da ake yadawa, Akwai dukan cututukan da zasu iya yadawa a Turai. Kuma muna da kyakkyawan tsarin yakar cututukan da kuma dakile yaduwarsu a nan. Wannan ya hada da tarin fuka da kuma cutar kanjamau.

Kasashen turai ne kadai daga cikin yankunan hukumar lafiya ta duniya da cutar kanjamau tayi Kamari, take kuma kara yaduwa musamman a gabashi. Jakab tace ‘yan ci rani da dama da suke dauke da cututukan sun kamu da su ne lokacin da suka shiga Turai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG