Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Gini Ya Ruguje A Kudancin Najeriya, Ya Kashe Mutum 3 Ciki Har Da Yara 2


Ma'aikatan ba da agaji gaggawa a lokacin da gini ya rufta
Ma'aikatan ba da agaji gaggawa a lokacin da gini ya rufta

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce wani coci ya ruguje a kudancin jihar Delta, inda ya kashe akalla mutum uku ciki har da yara biyu.

An ci gaba da gudanar da aikin ceto na ‘yan sanda da masu bayar da agajin gaggawa a cikin dare a wurin da cocin Salvation Ministries ke Asaba, babban birnin jihar Delta a kudancin Najeriya.

Masu ibada da dama sun taru ne domin yin hidimar ibada da yamma a cocin a ranar Talata a yayin da ginin bene mai hawa daya ya ruguje.

Jami’an ‘yan sanda sun ce an ceto mutane 18 daga wurin da lamarin ya faru, kuma an kwantar da su a asibiti, kuma uku daga cikin wadanda abin ya shafa na cikin mawuyacin hali.

Bayan sa'o'i kadan a ranar Laraba, hukumomi sun ce wadannan mutane uku sun mutu.

Hukumomi sun ce ana ci gaba da neman wadanda suka tsira.

A ranar Laraba ne hukumomin jihar Delta suka kaddamar da bincike kan abin da ya haddasa rugujewar ginin.

Rushewar gine-gine ba sabon abu ba ne a Najeriya. Daruruwan gine-gine sun yi ta rugurgujewa a kasar cikin shekaru goma da suka gabata, kamar yadda masana suka bayyana.

A watan Nuwamba, wani gini mai hawa 21 ya ruguje a Legas, inda ya kashe akalla mutane 45 – lamarin da ya kasance mafi muni a ‘yan shekarun nan.

Lamarin da ya haifar da sabon fargaba kan matakan gine-gine a kasar, inda kwararrun gine-gine ke zargin hukumomi da rashin bi da kuma aiwatar da ka'idoji yadda ya kamata.

Festus Adebayo, mai ba da shawara kan gine-gine, ya ce hukumomi sun yi jinkiri wajen daukar mataki.

“Mutane nawa ne aka kai gidan yari saboda lafin rushewar gini? Sai dai ayi surutai na mako guda kawai, bayan makon ya wuce sai a share lamarin.” Inji shi.

Rashin tsarin gine-gine da kuma kayan gini marasa inganci duk suna cikin matsalolin da ke tattare da rushewar gini.

A watan Nuwamba, hukumomin Najeriya sun yi alƙawarin musamman za su yi tsauri kan magina masu amfani da kayan da ba su da inganci.

Akwai karancin dakunan gwaje-gwaje don gwada kayan gini a Najeriya sannan kuma suna damasifan tsada.

Masana sun ce har sai an magance wadannan batutuwa, rayukan al’umma za su ci gaba da kasancewa cikin hadari.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG