Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Kwamitin Bincike A Amurka Zai Bada Bahasi Gameda Ikon Shugaban Kasa Akan Makaman Nukiliya


Shugaban kwamitin harkokin kasashen ketare na majalisar dattijan Amurka Bob Corker, ya sanar da cewa kwamitinsa zai saurari bahasi mako mai zuwa kan ikon shugaban kasa na amfani da makaman nukiliya.

Corker yace wannan zaman yana daga cikin matakan da majalisa zata dauka na nazarin ikon da Amurka ke da shi, da kuma hanyoyin amfani da makaman nukiliya. Yace majalisa bata sake waiwayar wannan ba tun alif da dari tara da saba’in da shida, ya kuma ce lokaci ya yi da ya kamata a sake nazari a kai.

Muhawara kan wanda yake da ikon bada izinin amfani da makaman nukiliya ya taso ne a majalisa bayanda shugaba Donald Trump ya yi barazana a cikin watan Agusta cewa, Koriya ta arewa tana iya fuskantar martanin da duniya bata taba gani ba, idan ta cigaba da ayyukanta na nukiliya.

Corker, wanda ya sanar da cewa ba zai sake tsayawa zabe ba a shekara ta dubu da biyu da goma sha takwas, ya yi sa’in-sa da shugaba Trump a bainar jama’a lokuta da dama a watan da ya gabata.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG