Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu Bakin Hauren Da Su Ka Nemi Arcewa Cikin Teku


Bakin Haure
Bakin Haure

Wasu bakin hauren da su ka zaku, sun yi ta tsalle daga wani jirgin ruwan Spain da ya ceto su, su na fadawa cikin tekun Bahar Rum jiya Lahadi a yayin da jirgin ruwan Spain din mai suna Open Arms ke kokarin neman tasha marar hadari da zai tsaya.

Bakin hauren sun yi ta tsalle zuwa cikin tekun suna ta iyo su na dosar Tsibirin Lampedusa na kasar Italiya. Sai dai ma’aikatan jirgin na Open Arms, su ma sun yi ta abkawa cikin ruwan, su na ta binsu su na kamo su, sun a mai da su cikin jirgin.

Jirgin ruwan na Open Arms mai dauke da bakin haure 107 ya tsaya daura da Lampedusa, yayin da ministan cikin gidan Italiya mai tsananin ra’ayi akan bakin haure, Matteo Salvani, ke ci gaba da kin barin jirgin ruwan ya isa tashar. Jirgin ruwan na Open Arms ya shafe kwanaki 17 a cikin teku.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG