Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'yan bindiga a Nijeriya sun kashe mutane 8 a wata mashaya


Wasu da hare-haren Boko Haram su ka rutsa da su

Wasu ‘yan Bindiga sun kashe mutane 8 a mashayar Nigeria.

Wasu ‘yan bindigar da ake zaton masu tsatsauran ra’ayin Islama ne, sun bude wuta da bindiga inda suka kashe mutane takwas, cikinsu harda ‘yan sandan Nigeria hudu a wata mashaya dake jihar Yobe-Arewacin Nigeria.

Rundunar ’yan sandan Nigeria ta aza laifin shirya kai harin na daren jiya Talata, a kan ‘yan kungiyar Boko Haram.Kungiyar da tayi barazanar halaka wadanda ba Musulmi ba dake zaune a Arewacin Nigeria inda Musulmi keda rinjaye.

Kungiyar ta Boko Haram ta kuma ci alwashin maida Arewacin Nigeria kasar Musulmi zalla.

A halin da ake ciki, Gwamnatin Nigeria ta baiwa ma’aikatan dake yajin aiki da zanga-zanga umarnin su koma bakin ayyukansu, im ba haka ba kuwa, ba za’a biyasu albashin su ba.

Idan za’a tuna, yau laraba aka shiga rana ta uku ke nan da ma’aikata ke yajin aikin da kungiyar Kwadagon Nigeria tayi kira da ayi domin nuna rashin yarda da janye tallafin farashin man fetur a Nigeria.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG