Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Tace Shugaba Jonathan Ba Zai Sami Galaba Akanta Ba


Imam Abubakar Shekau

Wani shugaban kungiyar Boko Haram yayi alkawarin kungiyarsa zata kai sabbin hare-hare, wan nan ikirarin yana kunshe ne cikin sakon da kungiyar ta saka a dandalin YouTube.

Wani shugaban kungiyar Boko Haram yayi alkawarin kungiyarsa zata kai sabbin hare-hare, wan nan ikirarin yana kunshe ne cikin sakon da kungiyar ta saka a dandalin YouTube.

A sakon na tsawon minti 15 da aka gani a dandalin Youtube, shugaban wani reshen kungiyar Imam Abubakar Shekau, wadda ya gabatar da jawabin, yana cewa mayakan kungiyarsa zasu ci gaba da kashe mutane kuma suma a shirye suke a kashe su domin suyi shahada.

Shekau yace shugaba Goodluck Jonathan wadda ya sha alwashin murkushe kungiyar ya girka yaki da ba zai sami galaba ba. Shekau yace tsarin mulki da emokuradiyy da Najeriya take bi ya sabawa addini. Yace a shirye Boko Haram take ta shiga shawarwari amma bisa sharadi data shimfida.

Ahalin da ake ciki kuma wuni na uku a jere dubban ‘yan Najeriya masu zanga-zangar suka fito domin bayyana fushinsu kan tsadar kudin mai, yayinda kugiyoyin kwadago na ma’aikata a sashen hakar mai suke shawarwarin ko su fada yajin aikin.

Aika Sharhinka

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG