Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda 'Yan bindiga Suka Kashe Mutum 8 Tare Da Yin Garkuwa Da Wasu Gommai A Jihar Neja


Wani yanki da 'yan bindiga suka hari a Najeriya

Rahotanni daga jihar Nejan Najeriya na nuna cewa wasu 'yan bindiga sun kai harin da ya hallaka akalla mutum 8 tare da yin garkuwa da wasu da dama a jihar.

Bayanai dai sun nuna hare-haren guda ne aka kai a kananan hukumomin shiroro da kuma Rafi, kamar yadda Malam Jibrin Erana ya bayana wa Muryar Amurka.

Shi ma dai tsohon shugaban karamar hukumar Shiroron, ASP Yarima Abdullahi Mai Ritaya ya ce akalla mutane 8 ne suka rasa rayukansu a wannan hari.

A yankin karamar hukumar Rafi ma maharan sun yi garkuwa da gomman mutane daga kasuyen Tungan Bako, in ji wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa.

Haka zalika a karamar hukumar Mariga, rahotanni sun nuna cewa sojojin Najeriya hudu sun rasa ransu a wata arangama da 'yan fashin dajin.

Hukumomi a jihar Nejan dai sun tabbatar da kai wadannan hare-hare kuma suna daukar matakin shawo kan lamarin in ji sakataren gwamnatin jihar Nejan, Alh. Ahmed Ibrahim Matane.

Kawowa lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga rundunar 'yan sanda ta jihar Neja akan wadannan hare-hare.

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG