Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yajin Aikin Kungiyar NLC Ya Kawo Tsaiko A Fannin Ilimi


Kofar Shiga Wata Makaranta a birnin Kano
Kofar Shiga Wata Makaranta a birnin Kano

Yajin aikin da kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta fara a daren jiya litinin ya gurgunta harkokin karatu a makarantun gwamnati na jihar Kano. Makarantun sakandare dana kwalejojin ilimi mai zurfi da kuma Jami’o’i mallakar gwamnatin jihar da na tarayya sun kasance a kulle a yau talata.

Sai dai daliban wasu daga cikin makarantu masu zaman kansu a birnin da kewayen Kano na ci gaba da daukar darasi, yayin da harabobin wasu daga cikin makarantun ke kulle.

Kazalika, ma’aikatan gwamnati sun kauracewa ofisoshin su, saboda biyayya ga umarnin kungiyar kwadagon ta kasa. Baya ga haka bankunan kasuwanci sun rufe ofisoshin su, amma wasu kamfanoni masu zaman kansu sun bude domin gudanar da ayyukan su na yau da kullum.

Masu Zanga-zangar Lumana Ta NLC A Jihar Kano
Masu Zanga-zangar Lumana Ta NLC A Jihar Kano

A hannu guda kuma, ‘yan kasuwa na ci gaba da hada-hada a kasuwanni, yayin da motocin haya da sauran ababen hawa ke gudanar da zirga zirga a titunan kwaryar birnin Kano. Kazalika, masu gidajen mai na sayar da man ga masu ababen hawa.

A jihar Jigawa kuwa, gwamnan jihar ne Malam Umar Namadi ya gabatar da kasafin kudi na badi a gaban majalisar dokokin jihar, duk kuwa da cewa, baya ga yajin aikin kungiyar kwadaon ta NLC, yajin aikin ‘yayan kungiyar ma’aikatan majalisar dokoki na jihohin Najeriya wato PASAN ya shiga mako na uku.

Abuja, Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)
Abuja, Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)

Kungiyar ta PASAN na daka nata yajin aikin ne a fafutikar neman gwamnoni su aiwatar da dokar tabbatar da ‘yancin kudade ga majalisar dokoki na jihohi.

Jimlar naira biliyan 298.14 ne gwamna ya kudiri aniyar kashewa a shekarar kudi ta badi wato, 2024.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG