Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Arewa Mazauna Amurka Sun Yi Allah wadai Da Kashe-kashen Da Ake Yi A Arewacin Najeriya


Zanga-zangar Nuna Takaicin Rashin Tsaro A Jihar Nejan Najeriya
Zanga-zangar Nuna Takaicin Rashin Tsaro A Jihar Nejan Najeriya

“Ya zama wajibi a tashi tsaye a kawar da su ('yan bindiga,) domin kuwa sun zama wata babbar barazana ga rayuwar jama’a da makomar kasa baki daya.

Kungiyar ‘Yan Arewa mazauna Amurka mai suna Dangi USA, ta yi Allah wadai da kakkausar murya da abin da suka kira kazamar ta’asar da masu sata da yin garkuwa da jama’a suke yi a Najeriya.

Cikin wata sanarwa da ta rabawa kafofin sadarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada Labarai da hulda da jam a’a, Kabir Isa Jikamshi, kungiyar ta Dangi ta ce akwai sosa zuciya da bacin-rai sosai, yadda wasu bata-gari suke yin garkuwa da jama’a da karbar kudin fansa ko yin mummunan kisa ga mata, maza da yara kanana.

A ‘yan shekarun bayan nan shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar matsalar tsaro, lamarin da ya jefa al’umar yankin cikin halin kunci.

“Irin wannan ta’asa da barayin jama’a suke yi, yanzu ta zama wata babbar barazana da tsokana da ta wuce hankali, wadda bai kamata ta ba da wata damar sake zama teburin shawarwarin sulhu da masu aikata ta ba.” Sanarwar ta ce.

Wasu daga cikin gwamnonin yankin arewacin Najeriya a taron da suka yi a Kaduna kan al'amuran tsaro(Facebook/Gwamnatin Filato)
Wasu daga cikin gwamnonin yankin arewacin Najeriya a taron da suka yi a Kaduna kan al'amuran tsaro(Facebook/Gwamnatin Filato)

Sanarwar ta kara da cewa, babu wani abu da ya wakana ko aka taba yi wa wani a baya, da zai gaskata irin kazamin cin zarafin da barayin jama’a suke yi a halin yanzu.

“Ya zama wajibi a tashi tsaye a kawar da su, domin kuwa sun zama wata babbar barazana ga rayuwar jama’a da makomar kasa baki daya.

“Muna yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta sauke babban nauyinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Rashin tsaro yakan zama jiki ko kuma ya gagara ne kawai, a yanayin da babu gwamnati a kasa.

“Dan Allah mahukanta da shugabanni a Najeriya, ka da ku ba da kunya, ku farka, idan barci kuke yi, ku sauke nauyin talakawa da ke kanku.” Sanarwar ta kara da cewa.

Kungiyar ta kuma ba da shawara da a hanzarta kirkiro dokar da za ta baiwa kowane dan Najeiya mai san zaman lafiya, ‘yancin mallakar makami da zai kare kansa da iyalansa, a duk lokacin da wani bata-gari dake neman sace shi ko iyalansa, ya tunkare shi.

“Dole a sake lale, a dena sakin yawancin wadanda ake kamawa da aikata laihuka ba tare da an tuhume su, ko hukunta su ba.

Wasu 'yan fashin daji a arewacin Najeriya
Wasu 'yan fashin daji a arewacin Najeriya

“Ta daya gefe kuma, Dangi USA tana yin kira ga sauran jama’a da su san cewa akwai gudunmawa da za su iya bayar wa wajen tabbatar da tsaron kansu, ta hanyar tallafawa jami’an tsaro da mahimman bayanai.

Kungiyar ta kuma mika jajenta sakon ta’aziya ga iyalai da ‘yan uwa da suka rasa rayuka, ko dukiyoyinsu a sanadiyar wannan ta’asa da ‘yan bindiga masu satar jama’a suke yi. Muna jin takaicin abinda sauran ‘yan uwa a Najeriya suke ji ko fama da shi, gameda tabarbarewar rashin tsaro a kasar

Hukumomin Najeriya dai sun sha fadin cewa suna iya bakin kokarinsu wajen daukan matakan dakile ayyukan ‘yan fashin dajin, matakan da jama’a suke cewa ba sa tasiri.

A ‘yan kwanakin nan rundunar sojin Najeriya ta ce ta yi ikirarin kai samame da dama akan ‘yan fashin daji lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan bindiga da dama

Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar a tsakiyar Dismba, babban hafsan sojin kasar Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya nuna kwarin gwiwar cewa dakarunsu za su yi galaba akan ‘yan bindiga da suka addabi yankunan arewacin kasar.

XS
SM
MD
LG